Salihu Yakubu Al-Manaar, Malami makaryaci, ko jahili?

Daga Abdulmumin Giwa
Na saurari wani rahoto da sashen Hausa na VOA sukayi inda suka sanya muryoyin bangarori biyu da rahoton ya shafa amma sai kuma wanda yayi rahoton ya kara da muryar Salihu Yakubu na’ibin masallacin al-Manar wanda hakan ya nuna cewa an yi rahoton ne da wata manufa.
Daga cikin surutan da shi Salihu al-Manaar yayi ya ce wai yan’uwa Musulmi basu bin duk wata doka ta kasa, suna daga tutar wata kasa ta Iran ba ta Nigeria ba, kuma suna biyayya da wata kasar basa tare da yan Nigeria, Iran ke basu kudi.
Inda yace ba a bin duk wata dokar kasa bai kawo misali ba shaci fadi kawai yayi babu hujja. Kuma da yake jahili ne shi, bai fahimci banbanci tsakanin bin doka da yarda da doka ba. Da cewa yayi bamu yarda da dokaba sai dokar Allah da ba zance masa komai ba domin kuwa haka Musulmi ya kamata ya kasance, mai sallamawa dokar Allah. Shi a matsayinsa na wai malami yana zargin wanda ya dora dokar Allah sama da duk wata doka, tir. Shi kuma bin doka a kasa koda ba a yarda da shi ba dolene saboda tsarin da kasar ta doru a kai kenan. Saboda haka otomatikiyyan wanda duk ke kasan ko ya shigo kasan wannan doka yake bi ko ya yarda dashi ko bai yarda da shi ba. Saboda haka rashin yarda da doka ba shine rashin bin doka ba. Wannan ne ma yasa kaga mun shigarda karar azzaluman da kake neman yardansu kotun Nigeria don neman hakki. Wannan shine bin doka da oda sabanin almajiranku wahabiyawa yan boko haram da zasu dauki makami su shiga kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba. Kaga kenan ko ku baku kaimu bin doka ba amma bamu yarda da wata doka sama da ta Allah ba kamar yadda ku kuka yarda da dokar kasa a sama da dokar Allah ba.
Magana ta biyu da ka gabatar cewa wai in muna muzahara muna daga tutar wata kasa ba ta Nigeria ba ya bayyanaka a matsayin makaryaci. Muna daga tutocin munasabobin da mukeyine kamar Ashura da Maulid amma ba ta wata kasa ba. In kuma muna muzaharar nuna goyon baya ga yan Falastinu muna daga tutarsu ta intifada wadda kuma ake dagawa a ko ina a duniya don goya musu baya. A lokaci guda kuma sai a tambayeka ko laifine a daga tutar wata kasa a Nigeria? In ko laifi ne ashe masu laifin nada yawa domin kuwa yawancin makarantu da hotel hotel suna daga tutocin kasashe da dama a harabarsu. Mutane na sa tutar America a motocinsu da ma rigunan da suke sawa. Hakama tutar Saudiya duk kuna sawa a motocinku, sai wannan ya hana zama yan Nigeria? Babu kuma wata doka da ta hana mallakan tuta ko tambari saboda haka kungiyoyi na da tutocinsu da tamburansu. Bari in tambayi Salihu al-Manaar ko ka taba ganin tutar Iran kuwa? Tir, malamin zamani kenan, karya halal.
Sai kuma zancen cewa muna biyayya ga Iran bamu tare da yan Nigeria wanda wannan maganace shaci fadi da batayi kama da na masu hankali ba. Maganar jahilai yan tasha amma daga bakin mai da’awar Malanta. Kai dake bin masarautar Saudiya da shugabannin Nigeria da ke bin America, da yan Katolika da ke bin Vatikan ko Rome, da yan Agilika da ke bin Ingila, da yan kwallo da ke bin Ingila ko Spain ko yan Tarika da ke da alaka da Morocco ko Algeria, a tsukakkiyar kwakwalwarka kana so kace kowa ba dan Nigeria bane kenan tunda yana kishin tushen akidarsa. Wannan zargin in na jita a tasha anayinta ba zan kula ba amma ace wai Malami Tir anyi hasara.
Sai karyar da kayi cewa wai Iran ke bamu kudi, a matsayinka na malami da sai ka kawo hujjar haka. Amma ko azzaluman gwamnatin Nigeria sun kasa kawo hujjar haka ko da kwaya guda kuwa. Amma sai fadi suke wai Iran na ba da kudi. Ni yanzu da zance Saudiya ya ke baku Kudi ku rika raba kan Musulmi suna samarwa da yan ta’adda kudade ina da hujja. Meye alakarku da kungiyar IIRO ta Saudiya da ta gina muku masallatai da makarantu? Ba zargin samar da kudade ga yan ta’adda ne yasa aka dakatarda aikintaba? Har Ku da kuke ci da sha daga Saudiya kuna da bakin cewa ana ba wasu kudi daga wata kasa? Mayuwatan banza. In kun isa ku kawo hujja daya na wasu kudi da aka taba bayarwa daga Iran mu kuma za mu gaya muku kudin da Saudiya ta ba wasu a gwamnatin Nigeria don su kashe yan Shi’a. Munafunci bai dace da malamiba.
Daga karshe nasihata gareka Salihu al-Manar shine cewar Allah “Kada ka bari kiyayyarka ga wasu mutanene ya hanaka yi musu adalci, kayi adalci shine mafi kusa da taqawa”

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s